Bincike

Kalaman Sheikh Daurawa akan ‘yan nanaye basu da alaka da kamun da hukumar tace fim takeyi

Kalaman Sheikh Ibrahim Daurawa na cewa; Ana ta kama masu wakokin nanaye an bar masu barna da sunan addini suna zagin Allah” basu da alaka da siyasa ko kama yan fim da ake zargin hukumar tace fina-finan Kano takeyi.

DABO FM ta binciko tare da tabbatar da cewa; Kalaman Sheikh Daurawa, basu da alakar kusa ko ta nesa da aikin da Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano take yi na kama mawaka da yan fim a yanzu.

Sheikh Daurawa, yayi kalaman ne dai dai lokacin da yake amsa tambayar wani dalibi akan “Bambancin Waka da Wake.”

Bayan dogon bayani, malamin yazo kan gabar wakokin yabo, inda ya bada kissa akan wasu mawaka da ma’aikin Allah (SAW) ya dakatar da yin wakensu a lokacin da suka ce ambaci shi (Manzon Tsira (SAW)) a matsayin wanda yasan abinda zai faru gobe.

Wakilin DABO FM da ya halarci karatun da aka gudanar a masallacin Ansarussunnah dake Fagge ya rawaito malamin yana cewa; 

“Akwai hukumar tace fina-finai ai, tana kama wadanda suka saba ka’ida. To su wakokin annabi babu mai tace su?”

“Babu hukumar da zata tace yabon Annabi, ta tace irin kalmomin da ake gayawa Allah, ta kama masu wakoki da musu ladabi tayi musu bita ta koya musu yacce ake yabon.”

“Ana ta kama masu wakokin nanaye, ga masu barna da sunan addini, ga masu zagin Allah, ga wadanda suke fadawa Annabi (SAW) kalmomin da babu ladabi”

“Su yakamata a nusantar a gaya musu ga yacce akeyi.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu an mayar da sarakuna a Kano basu da wata daraja -Aminu Daurawa

Muhammad Isma’il Makama

Sanyi: Gwauraye masu kwanan Shago, yin matashi da Galan, wanka da Buta abin tausayi ne -Daurawa

Dabo Online
UA-131299779-2