An kashe wata ‘Yar Najeriya bisa laifin safarar kwaya zuwa kasar Saudi Arabia

Karatun minti 1

Hukumomi a kasar Saudi Arabiya sun kashe wata mata ‘yar Najeriya bisa aikata laifin safarar kwaya zuwa kasar Saudi Arabiya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP, ra rawaito cewa, an kashe matar ne tare da wasu kaza ‘yan kasar Pakistan da Yemen ranar Litini a birnin Makkah dake kasar.

AFP din dai ta rawaito cewa a shekarar da muke ciki, a kalla mutum 53 aka kashe a kasar ta Saudi bisa safarar kwayoyi.

Kasar Saudi dai tayi suna wajen yankewa mutane da dama hukuncin kisa, ciki har da masu fafutukar kare hakkin dan Adam da ‘yan ta’adda.

A bara ne ma kasar ta yi yunkurin yanke wa wata mai fafutukar kare hakkin mata Israa al-Ghomgham wacce aka yi amannar cewa ita ce ‘yar kasar Saudiyya ta farko da take fuskantar hukuncin kisa saboda ayyukanta na kare hakkin mata.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog