Kwankwaso yayi wa daliban Najeriya a kasar Indiya sha-tara-ta-arziki, a ziyarar da ya kai musu yau Talata

by Dabo Online
0 comments

Yau Talata, 02/04/19, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai ziyara jihar Rajasthan dake arewacin kasar Indiya.

Kwankwaso ya kai wa daliban da suke karatu a jami’ar Mewar dake  garin Chittogarh, inda ya gana da daliban tare da yi musu fatan alkhairi.

Da yake jawabi, Kwankwaso yayi kira ga daliban dasu dage wajen yin karatun nasu, kuma su maida hankalinsu wajen kare mutunci addininsu dama al’adarsu.

Daga karshe yayi wa daliban kyauta kudi dalar Amurka 3,500 kwatankwacin Naira Miliyan Daya da dubu dari uku, domin su dan saukakawa kansu wasu yan wahalhalun da suke ciki.


4ED7369F 9A4F 4D63 84CF 387D9D2B1F1F - Dabo FM

Mun zanta da wasu daliban da suke chan makarantar ta Maiwar, inda suka bayyana mana farincikinsu bisa ziyarar Kwankwason, tare da yi masa addu’ar fatan alheri.

C54E4AC9 D09D 4F52 8A68 ABCF53B9AD4F - Dabo FM

 

Bidiyon Kwankwaso a jami’ar Mewar
Latsa alamar Play domin Kallon bidiyon

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00