Labarai

An kwantar da gwaman Bauchi, Bala Muhammad a asibiti a birnin Landan

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, yana kwance domin neman magani a wani asibiti dake birnin Landan na kasar Burtaniya.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da mataimakin gwamnan kan labarai, Mukhtar Gidado ya baiwa manema labarai a jiya Lahadi, inda gwamnan ya aike da sako zuwa ga al’ummar jihar akan hukuncin da kotu koli zata yanke na kalubalantar zabenshi da jami’iyyar APC take yi.

Sai dai sanarwar bata bayyana rashin lafiyar dake damun gwamnan nan.

Sanarwar ta rawaito gwamnan yana cewa; “Yanzu haka ina kwance a asibiti a birnin Landan, amma mun yarda cewa Allah kadai ya ishe mu, kuma shi zai bamu nasara. Nasara tamu ce da izinin Allah.

Sanarwar ta kara jaddada kudurin gwamnatin na inganta rayuwar mutanen Bauchi tare da yin shugabanci cikin adalci da daidaito cikin mutunci.

Haka zalika, gwamnan ya godewa magoya bayanshi wandanda yace suke yin mubaya’a kan tsarukan da gwamnatin ta dauko na ciyar da jihar gaba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ganduje na cikin jerin gwamnonin dake fuskantar barazanar tsigewa daga kotun ƙare kukan ka

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2