Labarai

An mayar da gidan Mata masu zaman kan su katafariyar Islamiyya a Igabi

A wani abun san barka da yabawa ga karamar hukumar Igabin Jihar Kaduna, wani gidan mata masu zaman kan su ya zama katafariyar makaranta da za’a cigaba da koyar da kanan yara a bangaren ilimin zamani da na addini a yankin kasuwar Daji da ke cikin karamar hukumar.

Da yake jawabi wurin kaddamar da gidan, Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dr Shehu Idris, wanda Makaman Zazzau Alhaji Umaru Mijinyawa ya wakilta, ya gode ma Allah bisa nasarar da aka samu har aka sayi gidan daga hannun mamallakin ta, da sanadiyyar shi aka jima ana aikata miyagun laifuka a wannan gida.
Kuma ya bukaci mutanen yankin su godewa Allah saboda tsamo su da ya yi daga halin da suke ciki a baya

Ya jinjinawa Hakimin gundumar Igabi da sauran sarakunan yankin bisa namijin kokarin da suka yi har aka kai ga samun wannan nasarar.

Makaman Zazzau ya Kara da cewa, jami’an tsaro sun samu labarin cewa wasu na shirya makarkashiya ga sabuwar makarantar da aka bude, sai dai ya yi kashedi ga duk wani mai nufin wannan makaranta da sharri ya guji aikatawa domin sam hukuma ba za ta bari ba.

Shi ma da yake jawabin sa a wurin taron, Hakimin gundumar Igabi Alhaji Abdulkadir Iya Fate, ya ce, tun a shekaru da suka gabata, aka fara kokarin karbar wannan gida daga mamallakin ta domin tsaftace shi daga kazamai da suka jima suna aikata badala da ma sha’a a wannan yanki. Duk da an samu kalubale matuka a lokacin karbar gidan, amma bisa taimakon Allah da kuma shuwagabannin al’ummar yankin, aka kai ga gaci kuma aka siya wannan gida daga wurin mamallakin ta.

Ya kara da cewa, saboda kokarin amsar gidan, mutanen yankun sun yi zargin cewar za’a nakasa masu harkokin kasuwancin su, saboda yadda mutane ke shigowa daga garuruwa daban-daban domin aikata badala a gidan. Amma ya roke su cure wannan tunani a ran su kuma su sa a ransu cewa, yanzu ne ma za su samu dukiya tsaftatacciya da zai taimaka wurin habaka tattalin arzikin yankin.

A jawaban su daban-daban, Sheikh Dr Muhammad Aliyu da Sheikh Abubakar Jumare, sun yi addu’oi na musamman ga al’ummar yankin, kuma suka yi fatan aikin da suka yi ta zama sanadiyyar yafe kura-kuran da suka aikai a baya.

Sai dai ya godewa Allah bisa nasarar da aka samu kawo yanzu.

UA-131299779-2