Labarai

IGP: Za’a dauki ‘yan Sandan sa kai 50 a kowacce karamar hukuma

Mai girma shugaban Hukumar ‘Yan Sanda ta kasa, IGP Muhammad Adamu, ya bada umarnin gaggawa kan shirin community Police da ake kokarin fadawa a fadin kasar nan.

Shugaban ya baiwa Kwamashinonin ‘yan Sanda na kasa (CPs) da mataimakan su (ACPs) da kuma Baturen ‘yan Sandan kananan Hukumomi (DPOs) umarnin fara shirin tantance ‘yan sandan yankunan.

Shugaban yace dole ne su je su hada kai da shugabannin Gargajiya domin zaben mutane na gari a cikin tsarin.

Muhammad ya kara da cewa, su community Police ‘yan Sanda ne da suke karkashin Hukumar sa, kuma za su saka kaya irin na ‘yan Sanda, sai dai lambobin su za su bambanta da na ainishin ‘yan Sanda da ake da su.

IGP ya kara da cewa, za suyi aiki ne a yankin da aka dauki mutum. Sannan ayyukan su za su zama, lura da kananan ofisoshin ‘yan Sanda, taimakon gaggawa ga wadanda suka ga mu da wani hatsari, da kuma dakile wata karamar rigima a matakin na kasa.

Shugaban yace kowacce Karamar Hukuma an ba su dama za a dauki mutane 50 ne a fadin kasarnan.

Shugaban ya bada umarnin fara aikin tantance wa nan take.

Karin Labarai

Masu Alaka

Hukumar ‘Yan sanda zata dauki ma’aikatan wayar da kan Jama’a guda 40,000 – IGP Adamu

Dabo Online
UA-131299779-2