Labarai

An samu bullar cutar COVID-19 ta farko a karamar hukumar Sabon gari

Bayan gwajin da aka yi ga daya daga cikin wanda aka killace bisa harsashen yana dauke da cutar sarkewar numfashi a karamar hukumar Sabon gari, da ke Jihar Kaduna, Yanzu haka an tabbatar da mutumin ya kamu da cutar da kuma shi ne na farko a yankin karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar Injiniya Muhammad Usman ya tabbatarwa Dabo FM da samun mai dauke da cutar.

Ya ce yanzu haka bisa bayanan da suka samu sun dauki wani mataki na wayar da kan al’umma domin tabbatar da cewar cutar bata watsu zuwa wasu sassan karamar hukumar ba.

Ya kara da cewa, zuwa yanzu an killace wanda ya kamu da cutar, kuma yana samun kulawar gaggawa daga kwararru da masana.

Bisa matakin ne ma, ya sa yanzu haka suka bazama zuwa bankuna da wuraren taruwan jama’a domin wayar masu da kai ta yadda za’a samu tsari mai kyau domin amfanin al’umma.

Muhammad Usman ya bukaci cigaba da amfani da shawar-warin likitoci da sauran masana kiwon lafiya domin ta haka ne kawai za’a kaucewa yaduwar cutar ta COVID-19.

Karin Labarai

UA-131299779-2