Fasahar Matasa Taskar Matasa

Ko kunsan hazikin matashin da ya zana fitaccen hoton Sarkin Kano murabus?

Hoton da kuke gani a sama, hoto ne da ya gama gari, ya kuma kayatar da mutane musamman masoya Sarkin Kano murabus, Muhammadu Sunusi II.

Sai dai mutane sun manta da gane matashin da ya zauna ya zana hoton da yakamata masoya Sarki mai murabus sunyi masa kyauta bisa namijin kokarin da matashin yayi.

Hoton ya ja hankalin mutane da dama musamman a lokacin da rikicin Sarkin mai murabus da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kara tsamarin da ya kai ga tsige Sarki Muhammadu Sunusi II.

Babban abin mamakin da ban sha’awa, shi dai wannan matashin bai wuce shekaru 19 zuwa 21 da daya ba.

A cikin shirin Taskar Matasa na DABO FM, mun zakulo matashi domin yaba masa bisa irin namiji kokarin da yake yi wajen yin zane mai kayatarwa da ban sha’awa.

Sunanshi Abbas Haruna Nabayi, dan asalin jihar Jigawa, mazaunin jihar Kano.

A tattaunawar da DABO FM tayi da matashin ya bayyana mana dan takaitaccen tarihinshi.

“Shekaru na 21, dan asalin jihar Jigawa, mazaunin jihar Kano.”

Matashin yayi zane-zane daban daban da suka yi fice. Ciki har da wanda yayi wa Alhaji Aliko Dangote, Naziru Ahmad, Ali Nuhu, Ahmad Musa da sauran fitattun mutane da ya hada da Larabawa da Turawan Yamma.

Ga wani rahoto da muka hada tin shekarar da ta wuce a kan matashin inda zaku ga zane-zane iri-iri da matashin ya dadi yana yi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Gidauniyar wasu ‘yan mata a Kano ta kai tallafin kayan abinci da tufafi zuwa gidan marayu da gidan yari

Dabo Online

Shawarata ga Shugaba Buhari kan yadda za’a magance tsaron Borno da Zamfara, Daga Datti Assalafiy

Dabo Online

Kwana 161 da daukewar tauye hakki da akayi wa matashi Abubakar Idris ‘Dadiyata’

Dabo Online

Hoton ‘soyayya’ na Baturiyar Amurka da dan Kano a dakin Otal ya janyo cece kuce

Dabo Online

Taskar Matasa: Abbas Nabayi, matashi mai zanen da yafi hoton kyamara

Dangalan Muhammad Aliyu

Ra’ayoyi: Bai wa diyarka jari, yafi kayi mata tanadin shagalin biki, Daga Idris Abdulaziz

Idris Abdulaziz Sani
UA-131299779-2