Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

An samu danyen Fetur a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya – NNPC

1 min read

Hukumar NNPC ta ayyana samun danyen Man Fetur a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Manajan hukumar ta rikon kwarya, Samson Makoji, ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa daya fitar ranar Juma’a.

Hukumar dai ta sanar da gano danyen man ne a Kogin Kolmani na biyu dake Benue Upper Trough, Gongola Basin ta yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Tin dai a watan Fabarairun 2019, shugaba Muhammadu Buhari, ya kaddamar da fara hakon duba man a yankin.

Mista Samson ya bayyana cewa; bayan doguwar haka da hukumar ta NNPC ta gudanar a tafkin, ranar Alhamis da misalin karfe 9:20 na dare, daya daga cikin durakun da aka ajiye domin tara ma’adanan da za’a hako, ta cika da Gas.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.