Labarai

An mayar dasu Kiristoci bayan yin garkuwa da su – Yara 9 ‘yan Kano da aka ceto a Onitsha

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana yacce tabi dindigi waje ceto Yara guda 9 yan jihar da akayi garkuwa dasu aka kaisu garin Onitsha na jihar Anambra domin yin aikin bautarwa.

Dabo FM ta tattaro cewa; Kwamishinan yan sandan jihar Kano, ya bayyana cewa rundunar ta samu kwararan bayanai a lokacin da take gudanar da bincike don ceton rayuwar Yaran.

“Tini dai munbi diddigi mun kuma samu nasarar cafke mutane 8 wadanda ake zargi su kwararru ne wajen sace-sacen Yara da yin cinikayyarsu ta hanyar safara dasu daga waje zuwa waje.”

“Mun ceto 9 daga cikin wadanda akayi garkuwa a garin Onitsha na jihar Anambra.”

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa daga wata majiya a cikin Jami’an tsaron cewa; An yiwa Yaran aski, an chanza sunayensu tare da addininsu na Musulunci.

Jaridar dai ta binciko cewa ana siyarda Yaran ga wadanda basu taba haihuwa ko wadanda suke neman Yara.

Haka zalika, Daily Nigerian, ta tabbatar da ganin wata takarda mai dauke da sunayen Yaran na asali wanda a yanzu haka daga cikin Yaran basa amsa sunayensu tin na asali.

Ta gano sunayen wasu Yara, Umar Faruq Ibrahim – Mai shekaru 10 da kuma Aisha Muhammad Abdullahi mai shekaru 9, wanda a yanzu suke amsa sunayen Onyedika Ogbodo da kuma Ozioma Ogbodo.

Tin dai a tsakankanin shekarar 2014-2019, wasu mutane suka shigar da korafin matsalar satar Yara da tayi tsamari a cikin jihar Kano.

Ana dauke Yara dayawa da shekarunsu ya basu wuce shekara 2 zuwa 6 wadanda ba’asan suwaye suke sace su ba, ba kuma asan ina ake kaisu ba.

A ranar 11 ga watan Satumba, yan sanda suka cafke wani Paul Owne da wata Mercy Paul da suke da zama a unguwar Dakata a lokacin da suke kokarin guduwa da wani Yaro, Haruna Sagir Bako da suka sace, zasu kaishi garin Onitsha ta jihar Anambra.

Paul Owne da Mercy Paul sun dai sace yaro Haruna Bako, a lokacin da yake kan hanyarshi ta dawowa daga makarantar Islamiyya a unguwar ‘Yan Kaba ta jihar Kano.

Masu Alaka

Jihar Edo: ‘Yan sanda sunyi arangama da masu sakawa mata yaji a al’aurarsu

Dangalan Muhammad Aliyu

Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kai hari Abuja, sun sace fasinjoji da dama

Muhammad Isma’il Makama

‘Yan Shi’a sun kashe mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Abuja

Dabo Online

Sojoji ne suka fatattaki ‘Yan Sandan da suka kama ni, suka sakeni na tsere – Dan Kidinafa

Dabo Online

#JusticeForKanoKids: ‘Yan sanda sun sake kubutar da Yaran Kano 2 daga Anambra

Muhammad Isma’il Makama

Rundunar ‘Yan Sandan Kano tace tana maraba da masu sha’awar shiga ‘Cell’ domin shakatawa

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2