Ra'ayoyi

Anyi kira ga Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II da ya janye kalamanshi akan satar Yara a Kano

Khalid Sunusi Kani, shugaban dalibai a Jami’ar Bayero dake jihar Kano, yayi kira ga Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, da ya janye kalamanshi akan satar Yaran Kano.

A makon da muke ciki ne dai Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, ya alakanta satar Yara 9 a Kano da sakacin Iyaye inda har ma yace yakamata gwamnati ta rika hukunta irin wadannan Iyaye.

Dalibin dake shekara ta 6 a fannin koyan Likitanci a Jami’ar Bayero ta Kano ya bayyana rashin jin dadinshi bisa kalaman Mai martaba Sarkin Kano.

A cikakken kalaman Matashin;

“A wannan karon, Sarki ya yi maganganu masu ban mamaki da ban al’ajabi, wanda muke ganin Sarki ya yi tuntuben harshe, ba haka ya kamata yace ba.”

“Sau da yawa mu mukanyi uwa da makar diya wajan wayar da kan al’umma. Amma a wannan karo bama tare da Sarki saboda yaci karo da tsarin mu’amalar rayuwa dama tsarin koyarwa ta addinin Musulunci.”

“Sanin kowa ne Annabi(S.A.W) yana fada a cikin wani sahihin hadisi yana cewa “Musulmi ya fadawa dan uwansa Musulmi magana me dadi sadaka ce”. Ni na dauka mai martaba Sarki zai fada musu maganganu masu nutsar da zuciya, ba kalaman da za su sa iyayen Yara jimami ba.”

Mai martaba sarki ya kamata yasan akwai bambanci tsakanin ‘Ya’yan talakawa da ‘Ya ‘yan masu kudi. A cikin talakawan ‘Ya yan su suna zuwa makarantu kama daga na Boko da na Islama, wanda sau da yawa yaran nan da kansu suke tattaki zuwa wadan can Makarantu sabanin abun yadda yake a gidan masu hannu da shuni.”

Ni dinnan zan iya tuno sadda muna yara muke zuwa Makarantar Firamare da Islamiyya a kafa. Wanda muke tafiyar kimanin kilomita shida (6) zuwa da dawo wa. Amma tun a lokacin ‘Ya ‘Yan masu kudi a mota ake kaisu. Saboda haka babu yadda shugaba zai zargi Iyaye da laifin barin yara suna fita daga gida. Ko kadan yin hakan ba dai dai bane.

Maganar da mai girma Sarki yayi ka iya tsunduma Iyayen Yara su fada zuwa cutar damuwa da tunanunnuka (depression). Wanda ba karamar illa bace a garesu. 

Amma inason mai karatu ya fuskanci zance na ba ina nuna iyayen yara basu da laifi ba. Suma iyayen yara ya zama dole su kula da ‘Ya ‘yan su sosai.

Muna kira ga mai martaba Sarki da ya yi gaggawar bawa jama’ar jihar Kano hakuri musamman iyayen yaran da suka salwanta.

Allah ya bayyana mana su, Allah ya kiyaye gaba, ameeen.

Khalid Sunusi Kani

52ND SUG PRESIDENT BUK

LEVEL 600 MEDICAL STUDENT

Email: kha[email protected]

Phone Number: 07030631259

Rubutun Matashin ne ba Dabo FM ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

#JusticeForKano9: Shirun ‘Yan Arewa da Malaman ‘Social Media’ akan mayarda Yaran Kano 9 Arna

Dabo Online

Su Waye ke bautar da Matasa a manhajar Facebook?

Idris Abdulaziz Sani

‘Idan Malamai na Allah basu farga ba, shedanun malamai za su cefanar da Musulunci’

Dabo Online

Ba Kwankwaso ne basa so ba, cigaban Talaka ne yake musu ciwo – Dangalan Muhammad Aliyu

Dabo Online

‘Yan siyasa na amfani da kalmar “Hassada” ko “Bakin ciki” don dakushe masu musu hamayya

Dabo Online

#Xenophobia: Abin kunya ne shugaba Buhari ya ziyarci kasar Afirika ta Kudu – Usman Kabara

Dabo Online
UA-131299779-2