Ba a ga wata a Indiya ba, Juma’a 1 ga watan Shawwal.

Karatun minti 1

Kwamitin ganin wata a kasar Indiya mai sunan Markazi Chand Farangi Mahali da ke karakshin kulawar Maulana Khalid Rasheed, ya ce ba a ga jinjirin watan Shawwal a kasar ba.

Majiyar DABO FM ta rawaito cewar malamin ya sanar da ranar Juma’a a matsayin daya ga watan Shawwal na shekarar 1442.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmin kasar da su tashi da azuminsu na 30 a gobe Alhamis.

An fara azumi a kasar a ranar 14 ga watan Afrilun 2021.

Kazalika, DABO FM ta tattara cewar; ba za a gudanar da sallar idi a kafatanin kasar ba sakamakon cutar Kwabid-19 da ta ke ta hallaka al’ummar kasar kamar yadda hukumar lafiyar kasar ta bayyana.

Gwamnatin jihar Maharashtra da ke kasar, a sakonta na taya Musulmi murnar Sallah karama, ta yi kira ga Musulmi da su yi sallolinsu a gida ba tare da zuwa ko ina ba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog