Sheikh Dahiru Usman Bauchi, jagoran darikar Tijjaniyya ta Najeriya, ya barranta da umarnin Sarkin Musulmi, ya jagoranci Sallar Idi a jihar Bauchi a Najeriya.
A jiya Juma’a, mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da rashin ganin sabon watan Shawwal a Najeriya, yayi umarnin tashi da azumi na 30 a ranar Asabar.
DABO FM ta tattara cewar bayan sanarwar Sarkin Musulmi, Sheikh Dahiru Bauchi ya sanar da ganin wata tare da kiran mabiyansa da suyi Sallar Idi a yau Asabar.
Cikin wani faifan bidiyo da DABO FM ta samu, ta hangi Sheikh Dahiru Bauchi yayin da yake gabatar da Sallar Idi a gidanshi na jihar Bauchi wanda wani daga cikin ‘ya’yanshi ya limancin sallar.