Home AzumiYanzu-yanzu: Babu kyakkyawan rahoton ganin wata a Najeriya – Kwamitin ganin wata

Yanzu-yanzu: Babu kyakkyawan rahoton ganin wata a Najeriya – Kwamitin ganin wata

by Dabo Online
0 comments

Kwamitin ganin wata a Najeriya, National Moonsighting Committee Nigeria, ya tabbatar da rashin samun cikakken rahotan ganin wata a fadin tarayyar Najeriya.

DABO FM ta tattara cewar kwamitin ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Twitter.

Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni da wasu kafafen sada zumunta suka yada cewar an ga jinjirin wata a jihar Bauchi da jihar Yobe a arewacin Najeriya.

Kazalika kwamitin yace mai alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Saad III zai yi karin bayani nan da wani lokaci.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00