Ramadan: Buhari yayi kira da a cigaba da wanzar da zaman lafiya, soyayya tsakanin al’umma

Shugaba Muhammadu Buhari yayi kira ga al’umma musulmi su cigaba da zama cikin lafiya da wanzar da soyayya a tsakaninsu.

A sakon taya musulmin kasar murnar zagayowar watan Ramadan ta hannun mai magana da yawun shugaban, Mallam Garba Shehu a jiya Lahadi.

Buhari yayi kira ga yan Najeriya da su saka Najeriya a cikin addu’o’insu domin cigaba da tabbatar da tsaro, kwanciyar hankali da zaman lafiya a Najeriya.

Yau dai Litinin, 6/5/2019, itace 1 ga watan Ramadan a kasar Najeriya dama wasu sauran musulman duniya, bisa shikashikan addinin musulunci, an umarci dukkanin musulmi azumtar watan baki daya.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.