Home LabaraiBabu wani Masallaci da aka ruguza a jihar Ribas – Gwamna Wike

Babu wani Masallaci da aka ruguza a jihar Ribas – Gwamna Wike

by Dabo Online
0 comments

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace Gwamnatin jihar bata rushe Masallaci kamar yacce ake ta yadawa ba.

Gwamnan ya bayyana labaran a matsayin na karya, ya kuma kalubalanci wadanda suke cewa an rusa Masallacin su fito su nuna inda aka rusa.

DABO FM ta tattaro cewa; Gwamnan yayi jawabin ne ta hannun mataimakin gwamnan a fannin kafafofin sadarwa, Simeon Nwakaudu, a yayin da ya ganawa da ‘yan Jarida a wajen da ake zargin gwamnatin da ruguza Masallacin.

Gwamnan yace masu yada labaran suna yi ne domin wata manufarsu ta daban wacce bata da kyau.

Ya kara da cewa; “Wasu manyan mutane a Najeriya suyi ta kirana a waya, suna fada min labarin karyar da yake ta yawo.”

“Yanzu dai gani da ku anan gurin, kunga babu wani masallaci anan.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00