Labarai

Bana cikin farin ciki, saboda talauci da rashin tsaron da ya addabi Arewa -Sanusi

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana babu wani shugaba wanda yasan me yake da yake cikin farin ciki da yanayin halin da Arewa ke ciki.

Majiyar Dabo FM ta bayyana Sarki Sanusi yayi wannan kalamai ne a ranar bikin cika shekaru 60 na gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Elrufai.

Sanusi yace “A duk inda aka taru bikin cika shekara, biki ne na farin ciki, amma satin daya wuce wani ya tambaye ni ko ina cikin farin ciki? Na bashi amsa da bana cikin farin ciki.”

“Furuci na ya bashi mamaki, Babu wani shugaba da zai farin ciki da halin da Arewa ta tsinci kanta na talauci da rashin tsaro, kashi 87% na talaucin Najeriya a Arewa yake.”

Sarki Sanusi ya bayyana idan har shugabanni basu farga ba wadannan matsaloli zasu rusa yankin Arewan baki daya.

Karin Labarai

UA-131299779-2