Labarai

Ra’ayoyi: ‘Rundunar ‘Shege-ka-fasa’ bata lokaci ne’

Idan akwai abu daya da mutanen mutanen Arewa, kususan ‘yan bokonsu suka kware da shi shine, yaudarar juna da kokarin biyan bukatar kai kawai.

Ba sai an yi sabon bayani akan halin da Arewa ta ke ciki ba, kowa ya san yanda masifar rashin ilimi, da rashin kasuwanci gami da ayyuka ga matasa ya gama mamaye duk wani sako da lungu na yankin. Amma kuma har yanzu an kasa ma fahimtar me yankin yake bukata da kuma hanyar da za a samar da shi.

Watan da ya shude, gamayyar kungiyoyi da kuma sarakuna hadi da gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya suka kaddamar da wata gamayya ko rundunar da za su inganta musu tsaro daga kalubalen da suka fuskanta. Duk da cewar da farko gwamnatin tarayya ta so ta taka musu birki, to amma saboda wayonsu da gogewarsu ta zarta ta shugabannin kasar na yanzu, daga baya aka ce an amince da su, har ma ana zancen za a yi gyaran fuskar kundin tsarin mulki don a samarwa da rundunar gurbi na doka a shari’ance.

Duk wata matsala ko tangarda da ta addabi Najeriya a wannan lokaci, daga Arewa aka kyankyashesu. Tun daga Boko Haram zuwa masu garkuwa da barayin dabbobi gami da masu jajayen kunnuwa, sai uwa uba rashin wayewar kai ta fuskar addini da zamani. Amma kuma abin haushi har yau an kasa zama a fadawa juna gaskiya a dauki matakan gyaran da suka kamata. Bari ku ji, Amotekun da Yarabawa suka kafa za ta yi tasiri da kuma biya musu bukatu.

Domin ga shi an fara koro ‘yan Okadar Arewa da ke Lagos. A sannu a hankali za su fara kafawa Fulani masu kiwo dokoki sai kuma sauran ‘yan Arewa da ke zuwa yankin neman kudi ko aikatau na masana’antu da gidaje. Amma kuma gamayyar Shege-Ka-Fasa kurarin shirme ne kawai. Siyasa ce irin ta matsorata da kuma wadanda ba su ma san me yankinsu yake ciki ba.

Yanzu da ace tun farko kungiyoyin Arewa sun samar da tsari na inganta rayuwar talakawa da marasa galihu ta fuskar inganta ilimi da kasuwanci da kuma zaman lafiya, da ba wani da zai tafi Lagos don aikata laifi da sunan samun kudi ko yin aikin wahala ya samu abin kashewa.

Yana da kyau duk wani da yake zaton shi wani abu ne a yankin Arewa, to ya mike ya samo wani mai tunani mai inganci irin na kawo ci gaba da tallafawa marasa galihu da tabbatar da adalchi, su yi rundunar da za su budewa gwamnati suka da shawarwari da za su inganta al’umma.

Maganar gaskiya sakaci da lalaci, gami da rashin bin doka da oda, sai zalunci da danniya hadi da wawaso akan dukiyar kasa, duk su ke kara tunzura al’umma, har ta kai jallin an fara aikata abubuwa ba daidai ba. Daganan ne sai kuma komai ya dagule a ma rasa ina za a dosa.

Daga karshe ina kira da hukuma da su daure su na cire siyasa ko son kai a kan duk wani lamarin tsaro, shari’ah da kuma addini hadi da lamarin zabe ko inganta rayuwar wadanda ake mulka!

Masu Alaka

Ra’ayoyi: Jahilci ne amfani da kalmar ‘Hassada’ a siyasa

Dabo Online

Meyasa wasu mutane suke jin tsoron tofa albarkcin bakinsu wajen kawo gyara a siyasa?, Daga Umar Aliyu Musa

Dabo Online

Su Waye ke bautar da Matasa a manhajar Facebook?

Idris Abdulaziz Sani

Shugabanci ne matsalar Najeriya da Arewa, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

#Xenophobia: Abin kunya ne shugaba Buhari ya ziyarci kasar Afirika ta Kudu – Usman Kabara

Dabo Online

Anyi kira ga Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II da ya janye kalamanshi akan satar Yara a Kano

Dabo Online
UA-131299779-2