Labarai

Bayan bayar da tallafin biliyan 4.3, Abdussamad BUA ya raba kayan abinci gida-gida a Kano

Abdussamad Isiyaka Rabi’u, shugaban kamfanin BUA, ya bayar da tallafin sama da biliyan 4.3 domin yaki da Koronabairas a Najeriya.

A karkashin gidauniyar BUA, ya na daga cikin wadanda suka fi baiwa Najeriya tallafin a yayin yaki da Koronabairas.

DABO FM ta tattara cewar da fari, BUA ya baiwa gwamnatin Najeriya Naira biliyan 1, daga bisani ya baiwa jihar Kano, biliyan 2, Legas biliyan 1 tare da kwamitin dake yaki da cutar na Najeriya naira miliyan 300.

A cikin wani faifan bidiyo da gidauniyar ta fitar, ta nuna yadda suka rika bi gida-gida a birnin Kano suna rabon kayayyakin abinci.

A bidiyon da DABO FM ta shaida da idanuwanta ya nuna yadda BUA ya raba abinci a wasu unguwannin na jihar Kano.

Unguwannin sun hada da Bridget, Gama da sauransu inda kowanne gida yake samun kananun buhun kayan abinci iri-iri wanda kamfanin yake sama da guda 5, Mai da katon buredi.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a jiya Alhamis ya bayyana tallafin Naira miliyan dari dari ga jihohin Kaduna, Kwara, Ekiti, Rivers da Sokoto.

Karin Labarai

UA-131299779-2