Babban Labari Labarai

Sabon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ya karbi ragamar kama aiki

Sabon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Kabir Bala ya naimi hadin kan daukacin ma’aikata da daliban Jami’ar domin samun nasara a shugabancin sa.

Kabir Bala, wanda ya karbi ragamar shugabancin Jami’ar a wani kwarya-kwaryar buki da aka shirya domin mika ragamar shugabancin daga hannun mai rukon mukamin shugabancin Jami’ar Farfesa Danladi Amodu Ameh. Da hakan ke nuna farawar wa’adin mulkin sa a ranar 30 ga watan Afirilu na shekarar 2020.

Sabon shugaban Jami’ar, wanda ya yabawa tsohon shugaban Jami’ar mai barin gado Farfesa Ibrahim Garba, bisa namijin kokarin da ya yi domin daga darajar Jami’ar ta Ahmadu Bello.

Ya ce, Akwai bukatar yin aiki tukuru domin cigaba da zamanantar da Jami’ar da kuma samar da tsare-tsaren da suka dace, kasancewar ana amfani ne da tsarin da aka samar tun a shekarar 1982 lokacin jagorancin tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Ango Abdullahi.

Sannan ya yi alkawarin tafiya da kowwa ba tare da nuna ban-banci ba.

Da yake nasa jawabin, shugaban Jami’ar na ruko mai barin gado Farfesa Danladi Amodu Ameh, ya kwatanta sabon shugaban Jami’ar ne a matsayin mutum jan gwarzo wanda kuma yake da kwarewar tafiyar da Jami’ar ta kowacce fuska, a don haka ya bukaci daukacin ma’aikata su bashi cikakken hadin kai da goyon bayan da ya dace na tsawon lokacin da zai yi yana jagoranci Jami’ar.

Idan za’a iya tunawa dai, tun a ranar 22 ga watan Janairu wannan shekarar ne, hukumar gudanarwar Jami’ar ta amince da nada Farfesa Kabiru Bala a matsayin sabon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, bayan karewar wa’adin Farfesa Ibrahim Garba da ya jagoranci Jami’ar har karo biyu.

Karin Labarai

UA-131299779-2