Labarai

Bayan bada tallafin karatu a kwanakin baya, Hon Ibrahim Garba Umar ya sake bada tallafin Azumi

‘Yan siyasa da kungiyoyi da kuma shuwagabannin al’umma daga gundumomi 13 da ke karamar hukumar zariya ne suka amfana da tallafin kayan hatsi da suka hada da Shinkafa da taliya da makaroni daga tsohon dan takarar majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Zariya kewaye Hon Ibrahim Garba Umar Madalla.

Da yake kari haske game da rabon da aka yi, Hon Ibrahim Garba Umar, ya ce, rabon na azumin bana ya bam-banta da sauran da aka saba gudanarwa duk shekara, lura da halin da ake ciki. bayan da gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar takaita zirga-ziraga saboda cutar sarkewar numfashi ta Kwabid 19.

A cear shi, sanya karin al’ummomin ya zama wajibi lura da cewar ba ‘yan siyasa ne kadai ke da tsananin bukata ba a irin wannan lokaci.

Ya kara da cewa, zuwa yanzu an kammala raba dukkanin kayayyakin da aka tsara za’a raba a wannan lokacin ga wanda ake sa ran sun amfana.

Hin Ibrahim Garba, ya sake Kira ga alumma su yi amfani da wannan lokaci na Ramadana wurin yawaita ibadu da komawa ga Allah ko za’a samu sauki a halin da ake ciki.

Kuma ya sake nanata kudirin sa na cigaba da samar da irin wadannan kayayyakin ga al’umma,tunda ko a kwanakin baya an yi rabon makamancin wanann baya ga daukar nauyin karatun dalibai da biyawa wasu kudin rubuta jarabawa a makarantu daban-daban.

Da suke jawabai daban-daban, wasu daga cikin wanda suka amfana da tallafin kayan abuncin, sun nuna matukar farin cikin su da godiya ga Hon Ibrahim Garba Umar Madalla, saboda tallafin da ya basu a irin wannan lokaci. Kuma suka yi fatan cigaba da samun jagoranci na gari a dukkanin lamuran sa.

Karin Labarai

UA-131299779-2