Labarai

Tirkashi: Masu dauke da cutar Koronabairas sun yi garkuwa da ma’aikatan lafiya a Kano

Wata balahira ta auku a jihar Kano bayan da masu dauke da cutar Koronabairas suka yi garkuwa da likitoci da ma’aikatan lafiya a wajen da ake killace masu dauke da cutar dake Kwanar Dawaki.

Majiyar Dabo FM daga TheCable ta bayyana wannan rahoton ya auku ne a ranar Alhamis, tsohon shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar Kano, Aminu Muhammad ne ya bayyana hakan cikin wata hira da yayi a gidan radiyo.

Ya kara da cewa “Masu dauke da cutar sunyi garkuwa da likitoci 2 da nas 1 a lokacin da suke zagayen duba marasa lafiyar.”

“Sun kulle su na wasu awoyi.” Muhammed yayi kira ga jama’a dasu bada hadin kai wajen yakar wannan annoba data addabi jihar Kano.

Da muka tintubi shugaban hukumar yaki da cutar Koronabarus, Tijjani Husaini, ya bayyana bashi da masaniyar balahirar ta auku.

Zuwa yanzu dai jihar Kano nada masu dauke da wannan cuta kimanin 482, wanda jihar ce ta biyu a jadawalin jihohi masu dauke da annobar bayan jihar Legas.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: Mutane 12 sun sake kamuwa da Kwabid-19 a Kano, jumilla 21

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutane 2 sun sake kamuwa da Covid-19 a Kano, jumilla 3

Dangalan Muhammad Aliyu

‘Babu ranar dawo da cibiyar gwajin Kwabid-19 dake Kano’

Dabo Online

Yanzu-yanzu: An kara tsawaita dokar kulle a Kano na tsawon sati 2

Dabo Online

Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

Dabo Online

Kwabid19: Zamu gwada daukacin Almajiran Kano – Ganduje

Dabo Online
UA-131299779-2