BBC Hausa ta dage muhawarar data shirya a Kano

Sashin Hausa na BBC, ya bada sanarwa dage ranar da aka shirya domin gabatar da muhawarar ‘yan takarkarun gwamnan jihar kano.

An shirya gudanar da muhawarar ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairi 2019, wanda a yanzu za’a gabatar da shirin a ranar 02 ga watan Fabairu 2019

Dabo FM tayi nazari domin gano makasudin dage muhawarar.

“Ranar tazo dai-dai da ranar da shugaba Muhammadu Buhari ya zaizo jihar ta Kano, domin bude wasu aiyuka da kuma yakin neman zaben komawarshi wa’adi na biyu.

Masu Alaƙa  BBC Hausa na neman ma'aikata

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.