Labarai

Borno: Boko Haram ta yanka mutane 3, ta sace tafi da mutane 7

Rahotanni sun bayyana yacce wasu da ake zargin mayakan ta’addancin Boko Haram sun yanke wasu bayin Allah guda 3 a kan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu.

Majiyoyi daga jami’an tsaro wadanda suka bukaci boye sunayensu, sun bayyanawa jaridar Punch al’amarin ya faru ne tsakanin garin Jakana da Auno a ranar Alhamis da misalin 11:15 na safiya.

Wakilin jaridar ya samu cewar an yanke mutane guda 3 wanda aka bar gawarwakinsu guda ukun a gefen titi.

Haka zalika majiyoyin sun kara da cewar a wajen da mayakan suka yanke mutanen, sun kuma dauke mutane 7 ta karfi.

Wani ma’aikacin gamayyar kungiyar masu lura da harkokin sufuri a tashar gwamnati, wanda shima ya bukaci a boye sunanshi ya tabbatar da faruwar al’amarin ya kuma bayyana yacce direbobi suka rika ajiye motocinsu daga chan nesa don gudun rasa rayukansu.

A dai makon da muke ciki ne dai kasar Chadi ta janye jami’anta dake Najeriya guda 1200, lamarin da ya kara karfafar hare-haren kungiyar Boko Haram.

Karin Labarai

UA-131299779-2