Labarai

Duk namijin da yake kashewa budurwar sa kudi baya talauci -Babban Shehin Malami

Wani babban shehin malami kuma masanin zamantakewa a kasar Ghana, Counselor Lutterodt ya bayyana cewa duk namijin da yake son cimma buri a rayuwa to sai ya dinga yiwa budurwar sa ruwan kudi.

Rahoton Dabo FM ya bayyana Mr. Lutterodt ya furta hakan ne a wata tattaunawa da gidan yada labarai na Rainbow Radio.

Da yake karin haske Counselor Lutterodt ya kara da cewa mata suna dauke da albarka fiya da namiji, duk wanda yake basu kudi isassu bazai yi gararanba a wajen neman arziki ba.

UA-131299779-2