Labarai

Buhari ya fusata, yayi barazanar sanya dokar tabaci a Kano akan rikicin Ganduje da Sanusi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yace zai sanya dokar ta baci a jihar Kano saboda wutar rikicin dake tsakanin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi kamar yadda kwamitin sasanta rikicin ya bayyana.

Cikin wani rahoto da majiyar DABO FM tayi ido biyu dashi, wanda shugaban kwamitin, kuma tsohon shugaban Najeriya, Abdulsam Abubakar ya fitar. Kamar yadda jaridar TheCable ta aike mana.

Rahoton yace, tun bayan da aka bayyana wa shugaban Buhari sakamakon binciken kwamitin sasanta bangarorin biyu, Buhari ya zabi mutum 3 domin zuwa suja kunnen bangarorin kan cewa indai basu sasanta junansu ba take zai kaddamar da dokar ta baci a fadin jihar ta Kano, inda har yayi ikirarin bada jirgin sa domin tabbatar da sakon sa yaje kunnuwan shugabannin biyu.

Sai dai kuma duk wannan yana zuwa ne bayan mai afkuwa ta afku, tinda tini gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi gaban Kansas wajen tube rawanin sarkin, a farkon satin nan.

UA-131299779-2