Labarai Wasanni

Juventus: Kwana 3 da cudanya da sauran yan wasa, an samu daya daga ciki dauke da Coronavirus

Barazana ta cika kungiyar kwallon kafa ta Juventus bayan samun dan wasan bayan kungiyar dauke da cutar Coronavirus, wato Rugani wanda kuma Kwana uku da suka wuce dan wasan yayi cudanya da kafatanin Yan kwallon ciki har da zakaran kwallon duniya Cristiano Ronaldo.

Majiyar DABO FM ta bayyana cewa yanzu haka an shigar da Cristiano Ronaldo da sauran yan wasan kungiyar wajen da aka kebe dumin duba masu dauke da cutar, kuma rahotannin da suka ishe mu har yanzunnan ana Kiran sakamakon ko shima Yana dauke da cutar.

Satin daya wuce an tabbatar wasu Yan wasa sun kamu da cutar a kungiyar kwallon kafar ta Juventus Wanda suke rukuni na biyu. Kamar yadda Goal.com ta bayyana. Hoto daga Football Galaxy.

UA-131299779-2