Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aike wa majalisun Najeriya wata doka da za ta bayar da damar a cefanar da kamfanin da yake samar da mai na gwamnati ga ƴan kasuwa.
Rahoton Dabo FM ya bayyana shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan ne ya tabbatar da samun kudirin wannan bukata daga gwamnatin tarayya, kuma ya ce majalisun biyu za su duba wannan buƙata.
Kazalika gwamnatin ta nemi majalissa ta bawa gwamnati damar kashe hukumar PPPRA da take kula da farashin mai a Najeriya.
Gwamnatin na son a yi wa sabon kamfanin sunan Nigerian National Petroleum Company (NNPC) a lokacin da za a yi rijistar idan an kammala bai wa gwamnati kadarori da kudaden kamfanin a cikin watanni 6.
Haka kuma a cikin kudirin, Gwamnatin tarayya ta bukaci Minisitan man fetur da ta kudi da su zauna su tattauna yadda za a rarraba hannayen jari a sabon kamfanin.
Tuni dai aka yi ta shan tata-burza a kan wannan buƙata a gwamnatocin baya da suka shuɗe na wannan buƙata musamman a lokacin shugaba Obasanjo.
Wannan na zuwa ne bayan zargin da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ya sha na cewa zai cefanar da kamfanin idan ya zama shugaban ƙasa, wanda masana na ganin zargin ya yi tasiri a faɗuwarsa zaben 2019.