Labarai

Bankuna zasu fara cire bashin da suke bin mutane a duk asusun bankin da sukayi ajiya – CBN

Babban bankin Najeriya CBN ya amince wa bankunan kasar nan cirar bashin da suke bin mutum a kowanne banki da yake da asusun ajiya.

Wannan dai doka ce da ta jima ta jiran amincewar Babban banki.

Jaridar Daily trust ta rawaito cewa, Yanzu idan mutum ya ci ba shi a wani asusun, ya tsallake yake ajiye kudi a wani asusun za ai amfani da lambar da ake kira BVN wajen janyo bashin da ya ci a biya banki, Kamar yadda sukai yarjejeniya tun farko.

Wannan dai abu ne da ya jima yana ciwa bankunan Najeriya tuwo a kwarya,domin sai mutum ya ci bashin banki, ya tsallake ya je ya bude asusun ajiya a wani bankin ba tare da ya jiya wancan bashin ba in ji CBN.

Wannan amince wa dai an yi ta ne jiya, bayan gudanar da zaman na musamman da bankunan kasar nan suke yi da CBN na watan Okotoba.

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman, Alh. Ahmed Abdullahi wanda yake Darekta ne a babban bankin Najeriya yace, sun baiwa bankuna wannan damar ne don ceto su, Daga hannun masu irin wancan halayya.

Mr Ebenezer Onyeagwu Manajan Bankin Zenith, ya yabawa wannan tsari, in da kuma ya tabbatar da cewa wannan tsari zai habaka tattalin arzikin Bankunan kasar nan. Ya kara da cewa, Yanzu babu wani batun kai korafin wani ko kararsa, hanya ce mai sauki, da mutum zai biya bashin da ya ci, cikin ruwan sanyi.

Comment here