Labarai

Talauci ke haddasa rashin zurfafa karatun Matasa a Yau – Ibrahim Garba Umar

Wani Matashi, kuma mai sharhi a kan lamuran Yau da kullum, Kana Magatakardar Kwalejin koyar da kiwon lafiya ta Madalla da ke Tudun Wadan Zariya, Alh Ibrahim Garba Umar, ya bukaci Matasa su dukufa wurin kama sana’o’i da shiga a dama da su a fagen Siyasa da kungiyoyi da kuma naiman Ilimin zamani da na Addini.

Ya bayyana haka ne a zantawar sa da manema labarai a Zaria.

Ya ce, Matasa su ne kashin bayan ci gaban kowacce al’umma, da kuma suke da kaifin basirar samar da wasu hanyoyin kawo cigaba domin amfanar da kansu da ma kasar su baki daya.

Ya kara da cewa, idan aka yi maganar matashi, ba wai jinsin maza kadai yake nufi ba, harda jinsin mata, Kuma a matsayin sa na matashi, a koda yaushe yana jin haushi matuka idan yaga matashi bashi da Ilimi ko kuma bashi da sana’ar juyawa.

A cewar sa, a Yau babu wani abu mai muhinmanci fiye da Ilimi, wanda shi ne ke daura mutum ga turba na gaskiya matukar an yi shi kamar yadda ya dace.

Ibrahim Garba Umar, ya nuna damuwa kan yadda karatun wasu matasan kan tsaya da zarar sun kammala makarantar sakandare, wanda ya kwatanta talauci a matsayin jigo na rashin cigaban karatun.

Ya bukaci gwamnati ta bullo da hanyoyin saukakawa ga yaran marasa galihu, domin su ne abun ya fi shafa.

Ya yabawa gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufai, bisa sanya yaron sa a makarantar gwamnati, kuma ya bukace shi ya tilastawa sauran mukarraban gwamnati, wurin sanya yaran su domin hakan ne zai gyara tsarin.

Da ya juya ga Matasa a Siyasa kuwa, Ibrahim Umar, ya yi watsi da masu ganin matasa basu da rawar da za su taka a Siyasar Yau, har ya bayar da misalin shi kanshi da har ya fito aka fafata da shi a zaben shekar Dubu Biyu da sha Tara da ta gabata, duk da karancin shekarun sa.

Ya kuma roki Shugaban Kasa Buhari da gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-rufai, su cigaba da baiwa Matasa kaso mai dama na wakilci a gwamnatocin su.

Da yake amsa tambaya kan yiwuwan baiwa Matasa daman guraben karo karatu kuwa, ya ce, hakan ya dace kuma yana da kyau matuka, har ya bada misali da Makarantar da yake jagoranci, wanda matasa ne kashi 98 bisa Dari na masu karatu a ciki, saboda yanda aka saukaka masu da samar da hanyoyin koyar da su cikin sauki.

Daga nan, sai ya taya daukacin ‘yan Najeriya murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai na shekaru 59.

A karshe, ya rufe da kira ga masu jagoranci a kowanne mataki, su rika sanya tsoron Allah da kishin kasa da kuma ci gaban ta a gaba.

Masu Alaka

Rigar ‘Yanci: Abba Gida Gida ko Executive Mai Sinƙe?, Daga A.M. Fagge

Dabo Online

Sashin Jami’ar ABU Zaria ya baiwa Anas Umar mai hoton Sarkin Kano Sunusi II lambar yabo

Dabo Online

Shigar Malamai Siyasa ba matsala bane, daukar bangare ne matsala, Daga Umar Aliyu

Dabo Online

Ko Sarkin Kano da Ganduje sun shirya ya kamata a kammala bincike – Barr Abba Hikima

Dabo Online

Ra’ayoyi: Bai wa diyarka jari, yafi kayi mata tanadin shagalin biki, Daga Idris Abdulaziz

Idris Abdulaziz Sani

Rigar ‘Yanci: Dama nasan za’a rina, tallafin Ganduje wajen ruguza Ilimin ‘yan Sakandire, Daga Nazeef Touranki

Dabo Online
UA-131299779-2