(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kaduna: Rikicin tsige kakakin majalisar karamar hukumar Zariya ya kara tsanani, an garzaya Kotu

dakikun karantawa

Har yanzu rikicin shugabancin da ta barke a majalisar kansilolin karamar hukumar Zariya ta Jihar Kaduna na cigaba da ruruwa tun bayan da a kwanakin baya DABO FM  ta rawaito  yadda wasu kansiloli Takwas cikin Sha Uku suka sanar da tsige shugaban majalisar Hon Hashimu Bako daga kujerarsa.

Kwatsam ana wannan sai ga wata takarda ta fito da su kansilolin nan Takwas suka naimi kotun majestare da ke Chediya GRA Sabon Zariya ta tuhumi Hon Hashimu Bako Wadata bisa zargin da suke masa da yin amfani da takarda da hatimin majalisar ya amincewa bangaren zartaswar domin ciwo makuden bashi dagat bankin Zenith.

Kuma suka ce banda wannan, akwai abubuwa da dama da suke zargin shi Hon Hashimu da aikatawa.

Bayan zaman kotun ne da ya gudana a Laraba 14 ga watan Satumba 2020 sai manema labarai suka tuntubi lauyan masu kara Barr Dakta Hassan Bala, inda ya ce zaman da suka yi sun tsammanin za’a gabatar da kara ne sai lauyan wanda ake zargi ya gabatar da uzurin cewa kotun ba ta da hurumin sauraron wannn shari’an, Amma bangaren su sun bayar da nasu dalilai da ke nuna cewa kotun na da dama da hurumin sauraron karar. Kuma ya tabbatar da cewar za su cigaba da yin duk mai yiwuwa domin bin hakkin wanda suke ganin an danne masu hakki.

Shi ma a nashi jawabin, lauyan da ke kare wanda ake kara Barista Samaila Abdu ya ce, suna ganin zuwa yanzu dalilai da hujjojin da suka tattara shi ne kotun bata da hurumin sauraron irin wannan karar, kuma duk da sun naimi shi wanda ake tuhuma Hon Hashimu Bako ya gurfana gaban kotu, to amma bisa dama irin ta shari’a za’a iya cigaba da sauraron shari’a ba dole sai wanda ake kara yana kotu ba tunda yana da lauya mai kare shi.

Bayan dogon muhawara tsakanin lauyoyin, an dage sauraron karar zuwa ranar Ashirin da Biyu ga wannan watan domin cigaba da shari’ar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog