/

Zazzau: Sabon rikici na shirin ballewa bayan Iyan Zazzau ya maka El-Rufa’i a kotu

Karatun minti 1

Iyan Zazzau, Bashir Aminu ya maka Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i a kotu bisa naɗin Ahmad Nuhu Bamalli sabon Sarkin Zazzau.

Rahoton Dabo FM ya bayyana Iyan Zazzau ya shigar da ƙara a gaban babban kotun jihar Kaduna inda ya nemi kotun ta tabbatar dashi a matsayin wanda ya cika kowacce ƙa’ida na zama sabon Sarkin na Zazzau.

Ƙarar ta bayyana biyo bayan samun ƙuri’u mafi yawa da doka ta tanada daga masu zaban sarki na masarautar Zazzau, Iyan Zazzau shine mafi cancanta ya zama Sarkin Zazzau.

Idan baku mantaba ranar 25 ga Satumba masu zaben sarkin Zazzau ƙarƙashin jagorancin Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu suka aike wa gwamna El Rufai sunayen mutum 3 da suka fitar cikin goma sha ɗaya da ke neman sarautar.

Cikin sunayen sun haɗa da Iyan Zazzau, Bashir Aminu wanda ya samu makin cancanta na 89, sai Yariman Zazzau, Munir Jafaru mai maki 87, sai kuma dan sarki marigayi kuma Turaki Ƙaramin Zazzau Aminu Shehu Idris mai maki 53.

Bayan aikewa da sunayen ne daga bayan gwamnan Kaduna ya soke su baki ɗaya, inda ya ƙara wasu ciki harda sunan sabon Sarkin na Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli. Kamar yadda DailyNigerian ta fitar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog