Labarai

Coronavirus: Kasar Sin ta ayyana ginin Asibiti mai gadaje 1000 cikin kwanaki 5 kacal

Hukumomi a kasar China sun tabbatar da ginin sabon asibiti da zai dauki gadaje 100 domin samun damar kula da barkewar annobar ‘Coronavirus’ a lardin Wuhan na kasar.

DABO FM ta tattara cewar tini dai aka hangi manya manyan kayyakin aiki na zamani da ma’aikata masu yawan gaske sun fara aikin babu jinkiri.

Gwamnatin Lardin tace bada tabbacin kammala aikin asibitin cikin kwanaki 5 kacal, za kuma a fara aiki dashi a ranar 3 ga watan Fabarairu.

DABO FM ta tattara cewar ba wannan ne karon farko da kasar take gina asibiti cikin gaggawa ba, ko shekarar 2003, kasar ta China ta gina Asibitin SARS a lardin Xiaotangshan cikin kwanaki 6 bayan barkewar makamanciyar wannan cutar da ta hallaka mutane 800 a wancen lokacin.

Zuwa yanzu dai, mutane 41 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar da akafi ittifakin an samo tana daga jikin nama a wata kasuwa dake lardin Wuhan.

Tini dai gwamnatin kasar ta haramta tafiye-tafiye a kasar domin gudun cigaba da yaduwar cutar da ta riga ka shiga garuruwa 14 tare da haramta yin bukin sabuwar shekarar kalandar kasar ta China ta bana.

UA-131299779-2