Labarai

Gidauniyar Hadeeyatul Khair ta fara koyar da Sana’o’i da darussan ilimin a yanar gizo

Gidauniyar Hadeeyatul Khair Foundation ta fara koyar da sana’o’i da darussan rayuwa a kan yanar gizo-gizo ga masu bukata musamman marasa karfi ko wadanda suke kasa biyan kudaden koyar da sana’o’in a makarantu.

Shugaban gidauniyar, Mufidah Ibrahim Fari ce ta bayyanawa DABO FM a cikin wata sanarwa da ta aike mana.

Tace sana’o’in sun hada da koyar da Girki-girken zamani, Kwalliya, gyaran jikin Mata, Daukar Hoto da sauran sana’o’in zamani, tare da daukan darussan zaman aure kamar yadda ta bayyana.

“Zamu bada muhimmaci wajen bangarorin girke-girke, kayyakin ciye-ciyen zamani da, daukar hoto da koyar da zamantakewar gidajen aure.”

“Tini dai mun kulla yarjejeniya da kwararru a fanni girke-girke guda 15, malaman addini da likitocin mata domin matsalolin mata.”

Ko da take amsa tambayar DABO FM kan yadda masu sha’awar samun tagomashin zasu iya ruskarsu, shugaban ta bayyana cewa ga mazauna jihar Kano, zasu iya tuntubarsu a kan titin Jambulo (3rd Gate) a cikin birnin Kano.

Ko kuma a tuntubesu ta lambobinsu kamar haka; +2348147984704, +2348030609682, +2347068255776.

Wasu daga cikin ayyukan gidauniyar,

Masu Alaka

Gidauniyar Hadeeyatul Khair ta kaddamar da shirin ciyarwar azumi kyauta

Dabo Online
UA-131299779-2