Labarai

Covid-19: Hukumar wutar lantarki zata bada kyautar wuta tsahon wata 2 a fadin Najeriya

Hukumar wutar lantarki ta ‘DisCos’ na shirin bada wutar lantarki ta tsahon watanni biyu kyauta biyo bayan annobar cutar Coronavirus.

Majiya Dabo Fm daga TheCable take bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba ta bakin mai magana da yawun hukumar ta kasa, Sunday Oduntan.

Cutar Covid-19 dai ta fantsama a Najeriya ‘yan satikan da suka gabata inda har mutane fiye da 200 aka tabbatar sun kamu da wannan cuta, wasu daga ciki ma cutar ta kaiga rasa rayukan su.

Karin Labarai

UA-131299779-2