Labarai

Kwabid-19: Ya kamata gwamnati ta bari koda mutane 12 su yi Sallar Juma’a-Sheikh Comasi

Wani malamin addinin musulunci a Zariya, Sheikh Abdulhakamu Muntaka Comasi, ya shawarci gwamantin jihar Kaduna ta sake duba dokar kulle da hana sallar Juma’a da ta sanya a fadin jihar, domin barin mutanen da ba su wuce 12 ba su gudanar da sallar Juma’ar a kowwanne masallaci.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da Dabo FM a Zariya.

Ya ce, ko a zamanin manzon tsira Annabi Muhammad S.A.W, an fuskanci bala’in yunwa da ta sanya mutum 12 kacal suka sallaci sallar Juma’a a lokacin.
Kuma a cewar shi, mutum 12 bai sabawa umarnin hukumar NCDC ba na hana taruwan jama’a.

Da ya juya ga bangaren al’umma kuwa, Sheikh Abdulhakamu Comasi, ya bukaci su cigaba da girmama shawar-wari da umarnin gwamnati da na masana kiwon lafiya kamar rufe fuska da wanke hannu akai-akai da kuma daina cudanya da jama’a domin inganta lafiyar su.

Daga karshe ya rufe da rokon mawadata da masu hannu da shuni su yi wa Allah su rika taimakon na kasa da su saboda halin da kasa ke ciki.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: Mutum 2 sun kamu da Koronabairas yau a jihar Kano, jumillar 313

Dabo Online

Yanzu yanzu: An samu karin mutane 22 masu dauke da Coronavirus, jumillar 276 a Najeriya

Dabo Online

Covid-19: Matakan da gwamnatin Kaduna ta dauka shi ne mafita – Dakta Hussaina Adamu

Mu’azu A. Albarkawa

Yanzu-yanzu: Nasiru El Rufa’i ya kamu da Coronavirus

Dabo Online

Tsohon kwamishinan Kano da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari, ya kamu da Koronabairas

Dabo Online

Zamu aiko muku da kayyakin da zasu rage radadin zaman gida – Buhari

Dabo Online
UA-131299779-2