//

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun afka kan tawagar Sarkin Pataskum, sun kashe ‘yan tawagarshi 3

0

Yan Bindiga sun afkawa tawagar mai martaba Sarkin Pataskum, Alhaji Umaru Bubaram a kan hanyar titin Kaduna- Zariya.

Tini dai mutane 3 daga cikin hadiman Sarkin suka rasa rayukansu.

Rahotanni sun bayyana cewar Sarkin yana yin zagaye zuwa fadar sarakunan arewacin Najeriya a wani mataki na shirin bude wani babban masallacin Juma’a a garin Potiskum wanda aka tsara kaddamar a ranar 18 ga watan Janairun 2020, kamar yacce Daily Trust ta tabbatar.

Maharan dai sun farwa tawagar Sarkin yayin da yake tafiya zuwa birnin Zariya.

An tabbatar da faruwar al’amarin a daren ranar Talata na wayewar Laraba da misalin karfe 2 na dare a wuraren kauyen Fandatio, kusa da Maraban Jos.

Masu Alaƙa  An fanso dan Majalissar jihar Kaduna awanni kadan bayan anyi garkuwa da shi

Sai dai har yanzu ba’a gane ko yan bindigar sun kawo harin ne taka-mai-mai ga mai martaba Sarki domin majiyoyin sun tabbatar da maharan basu kyale wasu matafiyan ba.

Da yake tabbatar da lamarin, Sarkin Yamman Potiskum, Alhaji Gidado Ibrahim yace anyi gaggawar tafiya da Sarkin zuwan asibitin Barau Dikko.

Su ma a nasu bangaren, rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al’marin, sai dai tace zata yi karin bayani a sanarwar da zata fitar.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020