Zanga-zangar nuna damuwar kashe-kashe a zamfara.

Karatun minti 1

Zanga-zangar nuna damuwa da kashe-kashe ta gudana a  jihar zamfara dake arewacin Najeriya a karamar hukumar Tsafe.

An gudanar da zanga-zangar nuna damuwa da kashe-kashe da ake yi a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya.

DABO FM ta tattara cewa an gudanar da zanga-zangar a karamar hukumar Tsafe.

Rahotanni da dama sun nuna cewa wasu matasa, ‘yan gudun hijira maza da mata tare da kananan yara su ne suka gudanar da zanga-zangar, lamarin da ya kai ga toshe sun wata babbar hanya dake kai wa babban birnin Gusau tare da lalata wasu kayyakin gwamnati.

A kwanakin baya wasu mahara da ake zargin ‘yan bindiga da barayin shanu sun kai wa wani kauye hari, lamarin da ya yi rasuwar mutane da dama.

Kakakin  rundunar ‘yan sandan jihar,  DSP Muhammad Shehu, ya bayyanawa manewa labarai cewa sun kama wasu daga cikin masu zanga zangar.

Matasan sun gudunar da zanga zangar ne don su bayyana damuwarsu a kan halin ko in kula da suka anayi kan kashe-kashen da suke faruwa a Jihar, a cewar wani matashi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog