Labarai

Dalibar da ta rubuta ‘Abba Gida Gida’ a hijabi ta samu tagomashi daga mabiya Kwankwasiyya

Dalibar dai ta samu tagomashi ne biyo bayan rubutun ‘Abba Gida Gida’ da tayi a jikin Hijabinta a ranar da take kammala karatun ta na Sakandire a watan Julin shekarar 2019.

Dalibar da aka bayyana da Rafi’a ta fito ne daga unguwar Gama dake karamar hukumar Nassarawa cikin kwaryar garin Kano.

Hotunan dalibar ya baza ko ina a shafukan sada zumunta musamman Facebook, inda magoya bayan darikar Kwankwasiyya a siyasa suka rinka tuttura hotunan tare da yin mata fatan alkhairi.

DABO FM ta binciko cewa, Rafi’a ta fara samun tagomashi ne bayan da shararren mawakin nan Tijjani Gandu, ya bada shigiyar nemo masa Rafi’a domin yayi mata wakar murnar kammala Sakandire da tayi.

Daga nan ne mabiya Kwankwasiyya suka fara bada kayan alfanu wadanda suka hada da kyautar kujerar Umara, Waya kirar ‘Android’, Katifa, Atamfa, Kayan Sakawa, Hijabai, Buhun Shinkafa da Taliya, Tsabar Kudi harda wanda ya mika mata kokon bararshi na aure.

Ga dai wasu daga cikin irin rubutun tagomashin da dalibar ta samu; a gafarcemu bazamu iya kawo muku hotuna ba;

“Duk wanda ya san mahaifinta, ya sanar da shi cewa; na dauke mata masa siyan Katifar Auren ta, 6*6 in za’a hada ni da shi yanzu”Aminu Ladan Tofa

Nayi alkawarin Naira dubu 10 ga wannan daliba” – Alh Halifa Usman Ka’is.

Zan bata N5000” – Ahmad Ahmad

Zan dauki nauyin Karatun ta har zuwa inda take bukata” – Mujaheed Ibrahim Arzai

Kujerar Umara daga kamfanin Lbranta Travel and Tours Nigeria Limited.

Kyautar Naira dubu 50,000 daga Alh Yusuf Imam Ogan Oye wanda tsohon dan takarar majalissar jiha a karamar hukumsr APAPA dake jihar Legas, Hon Kamalu Abdullahi Ali ya joranci zuwansu har gidan su Rafi’a.

A gafarce mu, iya wadanda zamu iya kawo muku kenan.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kamfanin tafiye-tafiye ya tabbatar da bawa dalibar ‘Abba Gida Gida’ kujerar Umara

Dabo Online
UA-131299779-2