Dalilin da ya sa aka ji ni shiru – Mahmud Nagudu Tattausan Lafazi

Sahararren mawakin yaren Hausa, Mahmud Nagudu ya bayyana dalilansa na jinshi shiru da mutane musamman masoyansa sukayi.

Duk dai mai bibiyar wakokin fina-finan Hausa bai manta da waye Mahmud Nagudu ba, domin a shekaru 10 baya, yana daya daga cikin mawaka masu tashe a masana’antar Kannywood.

DABO FM ta binciko wata hira da mawakin yayi da jaridar Daily Trust inda ya bayyana cewa ba daina waka yayi ba, sai dai ya chanza salon wakokinshi wanda yace ya dena wakokin nanaye ya koma wakokin yabon Fiyayyen Halitta Annabin SAW.

“To maganar gaskiya ina nan, ba wani waje na tafi ba, sai dai abin da nake so mutane su sani shi ne, komai na duniya yana da lokaci.

Mutum a kan sa ya kamata ya canza salo saboda tafiyar zamani. Abin da na sani shi ne, na yi wakokin fina-finai da dama, amma ban samu daukaka a waka ba, sai da na yi albam din ‘Tattausan Lafazi’, wannan ta sa na canza wa kaina tsari, domin Manzon (SAW) ya ce duk abin da ya kai kololuwa to wata rana kasa zai yi, to sai na ga tun kafin lokacin gara na yi wa kaina tsari. Ba kuma daina waka na yi ba sai dai ba ni da lokacin zuwa situdiyo kamar da.

Furodusoshi na nema na in yi waka sai dai babu lokaci.”

Mahmud Nagudu ya kara da cewa ba’a dena yayinshi ba, shine da kanshi ya ja da baya.

“Da an daina yayina ai ba za a ci gaba da sauraro wakokina ba, duk da na ja baya har yanzu ana sauraron wakokina. Abin da na sani shi ne, na san wadansu a masana’antar, kuma na yi fice.”

Mahmud yayi tsokaci dan dalilan daya saka yayiwa sarkin Kano Muhammadu Sunusi II waka ya kuma bada tabbacin cewa yayi wakar ne tin kafin Sarki Muhammadu Sunusi ya zama Sarkin Kano.

“to a gaskiya ba na yi wa mutum waka sai na yarda da nagartarsa da kuma kamalarsa, kuma gaskiya ban yi masa waka a lokacin da ya zama sarki ba. Lokacin da ya zama danmaje ma ban yi masa ba, na yi masa waka ne tun yana gwamnan banki, shi ma don alakarmu da shi ne da kuma kannensa Shema’au da Bera’u suka bukaci in yi masa waka, kuma a lokacin babu wanda ya yi masa waka. Ni na fara yi masa waka.”

%d bloggers like this: