An kwantar da fitacciyar mawakiyar Hausa, Maryam A Baba da aka fi sani da ‘Sangandale’ a asibiti sakamakon matsananciyar rashin lafiya.
Da yake fitar da labarin, abokin sana’arta, jarumi Abba El-Mustapha, ya bayyana cewar; Likitoci sun samu nasarar yi mata tiyata.
Sai dai bai bayyana ciwon da yake damunta.
Kazalika da take tabbatar da labarin, kanwar mawakiyar, Zainab A Baba, ta ce mawakiyar tana samun sauki bayan an kammala yi mata tiyatar.