Dan majalissar Tarayya mai wakiltar kananan Hukumomin Gagarawa, Gumel, Maigatari da Sule Tankarkar a jihar Jigawa, Hon. Nazifi Sani Fulawa ya gwangwaje al’ummar mazabarsa da abin arziki. Dan majalissar an zabe shi ne a shekarar 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Wakilin Dabo FM, Rilwanu Labashu Yayari ya rawaito mana cewa, abin da Dan Majalissar yayi, ba a taba samun wani Dan majalissa yayi makamancinsa ba a jihar Jigawa.
Daga cikin abubuwan da Dan Majalissar ya rabar sun hadar da:
- 1. Motoci 20
- 2. Babura 100
- 3. Gidaje 3
- 4. Adaidaita Sahu 10
- 5. Keken Dinki 100
- 6. Injin Markade 100
- 7. Firji Babba 50
- 8. Injin Faci 50
- 9. Injin wuta na chaji babba 50
- 10. Kwamfuta 50
- 11. Manyan wayoyin Hannu 50
Tabbas da sauran ‘yan majalissu za suyi koyi da shi, to da an amfana an kuma samu raguwar ma su zaman kashe wando a gari. Gwamnan jihar Jigawa Alh. Muhammad Badaru Abubakar ne ya kaddamar da wannan gagarumin rabon kayan arziki a garin Gumel