Mun kashe wa Korona Naira biliyan 30.5 a wata 4 – Gwamnatin Tarayya

Karatun minti 1
Boss Mustapha - Sakataren gwamnatin Najeriya, shugaban kwamitin yaki da Kwabid-19

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta kashe kimanin Naira biliyan 30.5 daga watan Afrilu zuwa Yuli na wannan shekarar da muke ciki domin yaki da cutar Kwabid-19.

Babban Akantan Najeriya, Ahmad Idris ne ya bayyana haka. Ya ce kudin da aka kashe kudi yana daga cikin Naira biliyan 36.3 na jama’a da kuma wadanda aka ba wa gwamnati gudunmawa domin taimaka mata kan yakar cutar Koronabairas da ta addabi duniya baki daya.

DABO FM ta tattara cewar ya bayyana cewar yanzu haka akwai ragowar Naira biliyan 5.3.

Ahmad Idris ya fadi haka ne bayan Kungiyar rajin kare tattalin arzikin kasa da ganin an kimanta gaskiya, SERAP da wasu masu ruwa da suka nemi karin bayani kan yadda gwamnati ke kashe kudaden.

Cikin wata sanarwa da babban mataimakin Daraktan kungiyar SERAP, Kolawole Oludare ya fitar a ranar Lahadi, ya ce a martanin da Akanta janar Ahmad Idris ya fitar, ya nuna cewa kwamitin yaki da cutar Korona na shugaban kasa ya kashe kimamin Naira biliyan 22, jihohi 36 sun kashe biliyan 7 duk saboda yaki da Korona.

Kazalika a jawabin Babban Akanta, ya bayyana cewar rundunar Sojin Saman Najeriya sun kashe miliyan 877 wajen zirga-zirgar kayyakin aiki da sauransu, ‘Yan sanda sun kashe Naira miliyan 500 na siyan kayan kariya daga cututtuka yayin da ya ce an kashe Naira 17,865 a cajin banki.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog