Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Duk ma’aikacin da ba’abashi albashin ₦30,000 ba, ya kai kara gaban Ministan Kwadago

2 min read

– Dokar ta fara aiki nan take.

– Dole dukkanin ma’aikatun na gwamnati da masu zaman kansu su biya ma’aikatansu N30,00 mafi karanci.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannun amincewa da biyan mafi karancin albashin N30,000 a Najeriya.

Shugaban ya saka hannun ne bayan lokacin mai tsawo daya dauka kafin saka hannun.

A makwonnin da suka gabata da majalissar Dattijan kasa karkashin jagorancin sanata Bukoula Saraki ta amince da karin albashin zuwa N30,000.

Da yake jawani bayan kammala sa hannun shugaba Buhari, babban mataimakin shugaban na Majalissar Wakilai, Sanata Ita Enang yayiwa manema labarai karin haske.

Yace, “Zaku ga ina murmushi a madadin ma’aikatan Najeriya. Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dokar gyara kudin albashin ma’aikata.”

Masu Alaƙa  Nuna alhinin kisan wani dan Legas da shugaba Buhari yayi ya janyo cece-kuce

“Ya zama tilas ga kowacce ma’aikata a Najeriya ta biya ma’aikatanta albashin N30,00 a matsayin mafi karancin albashi.”

Sai dai Sanata Enang yace dokar karin albashin bai zama tilas ga ma’aikata wacce take da ma’aikata kasa da 25 ba.

“Dokar ta kuma bawa dukkanin ma’akacin da ma’aikatarshi ta bashi kasa da abinda dokar tace, to lallai yanada damar da zai nemi a cika masa kudinshi ko ya shigar da kara zuwa ga hukumar kwadago mafi kusa dashi.”

“Ina kiran ma’aikatan Najeriya su fito suyi murna da wannan tsarin, kuma su taya shugaba Muhammadu Buhari murna.”

A ranar ma’aikata, zamu fito mu nuna murnar mu tare da goyon bayanmu ga tsari  Shugabancin shugaba Muhammadu Buhari.”

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.