Labarai

Fiye da mutum miliyan 1 ne suka nemi aikin Npower a cikin awa 48 kacal

Ministar walwala da jin kai, Sadiya Umar Faruq ta bayyana fiye da mutane miliyan 1 ne suka nemi guraben aikin da hukumar ta bude na shirin Npower ajin C cikin awa 48 da budewa.

Majiyar DABO FM ta rawaito Ministar ta sanar da hakan ne a daren Lahadi, ta shafukan yanar gizo, shirin wanda zai nawa ‘yan shekaru 18 zuwa 35 damar aiki ya hada da masu zurfi dama marasa zurfin karatu ta shafin hukumar website.npower.fmhds.gov.ng.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa “Hukumar zata ci gaba da aiki da masana kimiyyar ta domin taimakawa matasan dake kokarin cika neman aikin shirin Npower.”

Karin Labarai

UA-131299779-2