Labarai

Buhari, Tinubu da makomar Siyasar Hausa-Fulani a Najeriya, Daga Sen Aliyu Madaki

Aliyu Sani Madaki

Tarihin siyasa a Najeriya ya nuna cewa,akwai rashin jituwa a siyasan ce,tsakanin Hausa/Fulani da Mutanan Kudu Maso Yamma (South West) wannan rashin jitiwa ya faru tun lokacin Jamhuriya ta Farko(First Republic)a wannan lokaci akewa su Akinnola(Premier na South West)ganin kamar sunci amanar yan’uwan su Yarabawa don su na goyan bayan jam’iyyar NPC, jam’iyyar da ake wa ganin ta Hausa-Fulani ce.

A tarishin siyasar Najeriya duk jam’iyyar da Hausa-Fulani sukeyi,to wannan jam’iyyar ba a yinta akasar Yarabawa. Wannan yasa mulkin siyasa a Najeriya ya zama kamar hamayya ce, tsakanin Hausa-Fulani da mutanan South West(Wato Yarabawa).

Wannan magana hakan ce ta faru a jahuriya ta biyu, sanda mutanen Hausa-Fulani suke jam’iyyar NPN su kuma Yarabawa suke UPN, kuma duk wanda yake Bayarrabe ya shiga NPN ake masa ganin kamar yaci amanar yan’uwansa Yarabawa. Wanna ne yasa ko sanda aka yi jam’iyyar PDP ta kuma tsayarda Obasanjo dan takara, amma a 1999 ba a zabe shi a Jahohin Yarabawa ba don, yan’uwansa sunai masa ganin a jam’iyyar Hausa-Fulani ya fito Takara.

Amma a Magana ta gaskiya, shi Bola Ahmed Tinubu yayi ta kokarin ganin an sami fahimta irin ta siyasa tsakanin Kabilarsa ta Yarabawa da Hausa/Fulani.A shekarar 2007, yayi kokari wajen a tsaida Atiku Abubakar Takarar shugaban kasa a jam’iyyar AC wadda yake jagoranta, sannan a shekarar 2011,ya sake tsayar da Ribadau Takarar shugaban kasa a jam’iyyar ACN dake jagoran ta.

Sanin kowane cewa Asiwaju Bola Tinubu ya bada babbar gudunmawa waje kafa jam’iyyar APC,sannan yayi iya kokarin sa wajen ganin Buhari ya zama dan takarar jam’iyyar APC a jihar Lagos inda akai primary election.Maiyuwuwa in banda kokarin Tinubu da amfani da damar yin primarily a Lagos,da Jagora na Sen Rabiu Musa Kwankwanso shine zaici zaben.

Jama’a musanman kabilar Hausa-Fulani su sani, sanda Tinubu yake ta wannan kokarin ganin anyi hadaka tsakanin Kabilarsa ta Yarabawa, Yan’uwansa Yarabawa su na ta gayamasa cewa ya guji hadaka da Hausa-Fulani, wai acewar su,mu maciya amana ne, a siyasance.Wannan batu na karanta sau da yawa.

Inna son mai karanta wannan rubutu ya sani, ni Aliyu Sani Madaki dan Jam’iyyar PDP ne, kuma dan Kwankwasiyya mai addu’ar Allah Ya bawa jam’iyyar PDP nasara a zaben 2023 kuma ya bawa Kwankwaso shugaban kasa.Mai karatu zai iya cewa, meya hada ni da matsalar Tinubu da APC.Dalilin wannan rubutu shi ne, mu guji yin duk abunda zai kawo rashin yarda da aminci acikin Kabilun Kasar mu NIgeria. Mu Hausa-Fulani da an sanmu da amana da gaskiya, da kuma ciki alkawari.

Abunda yake neman ya faru da Tinubu, ko kuma ya faru zai iya kawo rashin jituwa ta har abada tsakanin kabilar Yarabawa da Hausa-Fulani. Kuma zai iya shafar kowa da kowa,ako wace Jam’iyya. Kuma zai iya shafar ya’ya da jikoki. Sannan zai iya kawo rashin yarda da amincin acikin kasa da Kabilun Kasa baki daya.

Ni a matsayina, na dan Jihar Kano, kuma dan Kwankwasiyya Inna zargin Asiwaju Tinubu da bada gudunmawa wajen karbe mana zaben Governor da mukaci,amma wannan ba zaisa nayi shiru ba,innaga yan’uwana suna neman jawomun gabar har abada banya babu ruwana. Manya Jam’iyyar APC musanman kabilar Hausa-Fulani susan ramin da suke gina wa,yana da zurfi,kuma zai haifar da barna ta har abada.Wannan shiri na awulakanta Tinubu zaizo da matsala da tsada ta gaske. Wallahi da abun zai tsaya kan Tinibu ne,bazan magana ba,amma zai iya shafar dukkan Kabilun(Wato Hausa-Fulani da Yarabawa).

Daga karshen inna addu’ar Allah Ya tsare mu da Mugunji da Mugun Gani.Allah Ya kare mana lafiyar mu da mutuncin da imanin mu,amin.

Allah Ya bada ikon fahinta.

Rep Aliyu Sani Madaki

Karin Labarai

Masu Alaka

Ko dai a dawowa da Sultan alfarmarsa, ko ya zare hannunsa a komai, Daga Hassan Ringim

..

Zato Akan Buharin 2015: Na zata Buhari ba zai yi cuta ba, Daga IG Wala

Dabo Online

‘Idan Malamai na Allah basu farga ba, shedanun malamai za su cefanar da Musulunci’

Dabo Online
UA-131299779-2