Hukumar kare hadura da kashe gobara ta jihar Abia, kudancin Najeriya sun bada tabbacin tashin dobara a kamfanin Guinness.
Kamfanin dai ya kone kurmus lamarin da yake babu wani abun da zai moru a wannan kamfani.
Hukumar kashe gobarar jihar tace tayi iyakacin kokarinta domin na kashe wutar amma hakan yaci tura.
Kamfanin Guinness dai babban kamfani ne a Najeriya da yayi shura wajen yin giya.