Labarai Najeriya Wasanni

Mahaifiyar Ahmed Musa ta rasu

Mahaifiyar dan wasan gaban kungiyar Super Eagles ta Najeriya, Ahmed Musa ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Sarah Moses mahaifiyar dan wasan ta rasu ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairun 2019 a wani asibitin kudi dake babban birnin tarayyar Abuja.

Da yake bayyanawa a shafinshi na Twitter da Instagram ya bayyana alhininshi na rashin mahaifiyar tashi.

Kwana daya Kafin rasuwar mahaifiyar dan wasan, Ahmed ya wallafa hotonshi dana mahaifiyar tashi inda yake fatan samun warakar ta, inda a yau kuma tace ga garinku nan.

Ta rasu tabar ‘yaya biyar, Ahmed Musa da kannenshi mata guda hudu.

Karin Labarai

UA-131299779-2