Saurayi ya kashe kanshi bayan zargin fyade

Karatun minti 1

Asiwaju mazaunin garin Lagos ya kashe kanshi a wani hotal dake garin na Lagos da misalin karfe 12 na dare.

A cikin wannan makon matashi yasha matsin lamba a shafin twitter domin zarginshi da yiwa wata baiwar Allah fyade, lamarin da Asiwaju ya karyata faruwar al’amarin.

Shugaban kamfanin Asiwaju Royal furniture, Micheal Asiwaju wanda ake masa lakabi da Mike Cash ya bayyana damuwarshi akan yadda matasan Najeriya suka saka shi a gaba wajen zarginshi da aiki yace bai aikata ba.

A ranar 12 ga watan Janairu, 2019, matashin ya wallafa bayanai da suka nuni da cewa ya kusa barin duniya inda yace: Ina muku bankwana, zan mutu nan bada dade wa ba.

Rahotanni sun nuna cewa ya sha guba ne da saninshin a dakin daya kama a otal din dake jihar Lagos, Najeriya.

Shafin Asiwaju na Twitter
Shafin Asiwaju na Twitter

Ra’ayoyin matasa akan lamarin

Daga shafin Twitter
Daga shafin Twitter
Daga shafin Twitter

Karin Labarai

Sabbi daga Blog