GANDUJE
Labarai

Zaman kulle: Ganduje ya ba wa al’ummar Kano hakuri

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa al’ummar Kano hakuri sakamakon sanya dokar zaman gidan dole da gwamnatin tayi domin dakile yaduwar cutar Kwabid19.

Gwamnan ya yi wannan furuci ne a wajen addu’ar cikar shekaru 6 da rasuwar mai martaba San Kano mai rasuwa, Alhaji Dr Ado Bayero, wacce aka saba yi a fadar masarautar Kano.

DABO FM tattara cewar a Marigayi Ado Bayero ya rasu a ranar 6 ga watan Yuni a shekarar 2014 bayan shafe shekaru sama da 50 a kan karagar mulkin Kano.

Ganduje ya yi kira ga al’ummar Kano da su cigaba da yin da’a ga dokar zaman gida domin taimakawa wajen dakile yaduwar cutar ta KWabid19 a fadin jihar Kano, kamar yadda Kano Focus ta rawaito.

“Wannan annoba ta taba al’amuran addininmu, al’ada, tattalin arziki da zamantakewarmu.”

Ganduje ya kara da cewa; “Muna roko Allah Ya shafe mana da wannan cuta Ya kawo mana dauki.”

A nashi jawabin, Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga al’umma da su kasance masu da’a da umarnin gwamnati tare da bin shawarwarin masana kiwon lafiya domin taimakawa wajen dakile cutar ta Kwabid19.

Karin Labarai

UA-131299779-2